Gwamnatin Trump na shirin ƙulla yarjejeniyar saka jari da Ukraine

0
14
Gwamnatin Trump na shirin ƙulla yarjejeniyar saka jari da Ukraine

Gwamnatin Trump na shirin ƙulla yarjejeniyar saka jari da Ukraine

Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗa a ranar Juma’a cewa yana sa ran Ukraine zata amince da shawarar kulla yarjejeniya da zata hada da zuba jarin Amurka a albarkatunta domin taimaka Amurka ta fanso wasu tallafin tsaronta.

Muna sa ran sanya hannu kan wata yarjejeniya, nan da dan lokaci, wadda zata bamu tabbacin maido dala bilyan 400 zuwa 500,” Trump yana fadawa manema labarai a ofishinsa na Oval a lokacin da aka tambaye shi batun yiwuwar kulla yarjejeniyar.

Trump ya ce “Wannan babban al’amari ne kuma su ‘yan Ukraine suna bukatar haka, kana hakan zai sa mu kansance a cikin kasar,” inda ya kara da cewa “Zamu maido da kudadenmu.” Ya ce wannan wata jarjejeniya ce da ya kamata a kulla tun kafin ya karbi ragamar mulki.

KU KUMA KARANTA:Trump bai ƙara haraji nan take ba, kamar yadda ya yi alƙawari

Gwamnatin Trump ta bada shawarar kulla yarjejeniyar albarkatun karkashin kasa da ba a saba gani ba, wanda bangarensa mafi girma ya maida hankali kan yarjejeniyar kawo karshen yakin Ukraine.

Kalaman shugaban sun biyo bayan rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta gabatar wa da Kyiv wata sabuwar yarjejeniyar ma’adinai da aka sake shiryawa bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yi watsi da shawarar farko.

Mai ba Amurka shawara kan tsaron kasa Mike Waltz ya yi irin wadannan kalaman da safiyar Juma’a a taron masu bin akidar siyasa ta ‘yan mazan jiya na shekara-shekara a wajen Washington.

Leave a Reply