Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi alƙawarin cewa nan ba da daɗewa ba gwamnatin tarayya za ta shawo kan matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa saboda illar da take yi a harkar noma da abinci.

Shettima ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da tawagar Masarautar Haɗeja ƙarƙashin jagorancin Sarkin Haɗejia kuma shugaban majalisar Sarakunan gargajiya na jihar Jigawa, Alhaji Adamu Abubakar Maje, suka ziyarci fadar shugaban ƙasa a Villa, a Abuja.

“Ina so in isar muku da saƙon shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa za a saka ƙalubalen wurin a cikin kasafin kuɗi na gaba,” in ji shi.

A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya wajen samun duk wani ci gaba mai ma’ana a ƙasar.

Da yake jaddada mahimmancin zaman lafiya ga ci gaban ƙasa, Shettima ya ce zaman lafiya babban abin da ake buƙata shi ne ci gaban ƙasa, inda ya ce jihohin Kano da Jigawa sun kasance masu zaman lafiya da yawa kuma “tsibirin zaman lafiya ne a cikin tekun talauci da rashin tsaro da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

KU KUMA KARANTA: Jihohin Kogi, Anambara da Yobe za su fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a daminar bana – NiMet

Mataimakin shugaban ƙasan ya yabawa masarautar Hadeja bisa irin gagarumin goyon bayan da suke baiwa gwamnatin Tinubu/Shettima inda ya lura da cewa “kamar yadda a lokacin da muka je Hadeja, ba mu ke kan karagar mulki ba, kuma mai martaba ya nuna goyon bayansa a gare mu.

Babban goyon baya ne kuma an kafa shi a kan gaskiyar cewa ƙungiyarmu ita ce mafi kyau ga al’umma.

“Mataimakin shugaban ƙasa Shettima wanda ya yabawa Masarautar Hadeja kan ci gaban da ta samu, ya bayyana cewa “lokacin da na yi tattaki daga Kano zuwa Hadejia, wannan na daga cikin abubuwan farin ciki na.

Na ga ci gaba na tasowa, na ga jami’o’i sun taso, na ga wani kamfanin shinkafa na Aliko Dangote, na ga ƙoƙarin ci gaba da yawa”.

Tun da farko dai Sarkin ya taya Tinubu da Shettima murnar rantsar da su tare da alƙawarin ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya.

Yayin da yake gode wa mataimakin shugaban ƙasa kan naɗin ɗaya daga cikin ‘ya’yansu a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, ya yi addu’ar Allah ya yi masa jagora ga sabuwar Gwamnati.


Comments

3 responses to “Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima”

  1. […] Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *