Gwamnatin tarayya za ta gina tituna 14 a inda ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a ƙasar

0
56
Gwamnatin tarayya za ta gina tituna 14 a inda ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a ƙasar

Gwamnatin tarayya za ta gina tituna 14 a inda ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a ƙasar

Majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince da aikin gina tituna 14 da gadoji wanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Ekiti da Adamawa da Kebbi da jihar Enugu.

Ministan ayyukan, David Umahi ne ya bayyana hakan yayin yiwa manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayani bayan zaman majalisar zartarwar.

Ya ce sauran jihohin sun hada sa Cross River da Ondo da jihar Osun da Ebonyi da Abia da jihar Imo.

Ya ce, an bada aikin kwangilar gina hanyoyin ne kari kan kwangilar gyara gadar Gamboru dake Gamboru-Ngala da Kala-Balge a jihar Borno.

KU KUMA KARANTA:Za a yi babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya don iganta ci gaba

Minsitan ya ce majalisar ta kuma amince da sabuwar kwangilar gina hanyar Maraban-Kankara da Funtua a jihar Katsina.

Haka kuma, majalisar ministocin karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta amince da gina hanyar Afikpo zuwa Uturu-Okigwe a jihar Ebonyi da Abia da jihar Imo.

“Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da Naira Biliyan 80 don kammala wannan aikin, wanda jimilla ya kama biliyan 280.”

Leave a Reply