Gwamnatin tarayya ta ware ranakun hutu don bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

0
194

Gwamnatin tarayya ta bada hutu a ranaikun, Litinin 26 da talata 27 ga watan Disamban 2022 da kuma ranar Litinin 2 ga Janairun 2023 a matsayin ranaikun hutu domin bukukuwan Kirsimeti da da ranar bada kyaututtuka na Boxing Day da kuma ranar sabuwar shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Dr Shuaib M.L. Belgore, babban sakataren ma’aikatar, a ranar Alhamis.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin tarayya na neman gwamnoni su saki 30% na fursunoni a jihohi

A lokacin da yake taya kiristoci da ɗaukacin ‘yan Najeriya mazauna gida da na ƙasashen waje murnar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara ta bana, Aregbesola ya gargaɗi Kiristoci da su yi koyi da Yesu Almasihu a cikin ayyuka da kuma bin koyarwarsa, musamman a kan ɓangaskiya, bege da ƙauna.

“Dole ne mu sanya rayuwar Yesu Kiristi cikin ayyukansa da koyarwarsa akan tawali’u, hidima, tausayi, haƙuri, salama da adalci, wanda haihuwarsa ke nuna hakan.

“Wannan ita ce hanya mafi kyau don murnar Kristi da kuma bikin haihuwarsa,” in ji shi.

Ministan wanda ya jaddada cewa, zaman lafiya da tsaro abubuwa ne guda biyu masu muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki da wadata, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan da suka dace wajen yin addu’o’in kawo ƙarshen duk wata matsala ta rashin tsaro a ƙasar.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su tabbatar da zaɓen 2023 cikin nasara ta hanyar kaɗa kuri’a cikin lumana tare da kaucewa duk wani abu da zai iya lalata aikin ta kowace hanya.

Aregbesola ya bayar da tabbacin cewa gwamnati ta samar da ingantattun matakai na tsaron rayuka da dukiyoyi, ya kara da cewa gwamnatin tarayya na fatan ‘yan Najeriya za su goyi bayan ƙoƙarin hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu amfani da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu lura da harkokin tsaro, inda ya bukaci su kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da suke zargi da shi ga hukumar tsaro mafi kusa da kuma ta hanyar manhajar N-Alert na wayoyin Android da IOS.

Leave a Reply