Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ‘yan Najeriya akan su matsa daga gaɓar koguna

0
29
Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ‘yan Najeriya akan su matsa daga gaɓar koguna

Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ‘yan Najeriya akan su matsa daga gaɓar koguna

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar dake kula da kogunan ƙasar (NIHSA), ta shawarci al’ummomin dake zaune kusa da gabar kogin Benuwe da su gaggauta matsawa zuwa wuraren da basu da hatsari.

A sanarwar da ya fitar a yau Alhamis, babban daraktan NIHSA, Umar Muhammad, ya yi gargadin cewa yawan ruwan dake kogin Benuwe ya kai mizanin yin ambaliya saboda karuwar ruwan sama.

Haka kuma ya buƙaci mazauna kusa da kogin Neja dasu matsa zuwa wuraren da basu da hatsari kasancewar hukumomin gudanarwar madatsun ruwan Kainji da Jebba na kokarin shawo kan ruwan daga yin ambaliya.

A baya-bayan nan, gwamnati ta gargaɗi ‘yan Najeriya da su matsa zuwa wuraren da basu da hatsari sakamakon sako ruwan da aka yi daga madatsar ruwa ta Lagdo a jamhuriyar Kamaru.

KU KUMA KARANTA: Cutar kwalara ta ɓarke a Borno bayan ambaliyar ruwa da ta mamaye garin

Hakan na zuwa ne bayan da sakin ruwan da aka yi daga madatsar ruwa ta Alau ya hallaka fiye da mutane 30 tare da yin awon gaba da dubban gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Leave a Reply