Gwamnatin tarayya ta bai wa Rahama Sadau muƙami

Gwamnatin Tarayya ta naɗa fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau a matsayin mamba a kwamitin kula da shirin zuba hannun jari a fannin kirkire-kirkiren zamani (iDICE).a

Jarumar ce ta bayyana hakan a Yammacin wannan Alhamis ɗin cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook.

A cikin saƙon, Rahama Sadau ta miƙa godiya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima da ya ba ta wannan muƙami bisa la’akari da cancantarta.

Bayanai sun ce a Larabar da ta gabata ce mataimakin shugaban kasar ya ƙaddamar da kwamitin shirin iDICE wanda ke da alhakin lalubowa tare da tallafa wa mutane ko wasu kamfanoni da suke da wata fikira ta zamani musamman a ɓangaren tsare-tsare da dabaru a fannin sana’o’i.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya naɗa jarumi Ali Nuhu da wasu mutane 10 muƙamai

Rahama Sadau ta kuma bayyana cewa Shirin iDICE haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da hukumomin duniya da suka haɗa da Bankin Masana’antu, Bankin Bunkasa Afirka, Hukumar Bunkasa Faransa, da kuma Bankin Bunkasa Musulunci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *