Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin murnar da zagayowar ranar ma’aikata a Nijeriya.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.
Aregbesola, a wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shu’aib Belgore, a ranar Juma’a, ya yabawa ma’aikata bisa ƙwazonsu, da sadaukarwa, inda ya bayyana cewa ƙoƙarin da suke yi na da nasaba da ɗaukakar ƙasar nan da kuma girmama Nijeriya yanzu ya yi umarni a cikin kwamiti na al’ummai.
KU KUMA KARANTA: Albufeira, ƙauyen kamun kifin da ya zama baban wurin hutu a duniya
Ya ce, “Akwai mutunci a cikin aiki, dole ne mu kasance da himma da jajircewa kan aikin da muke yi domin yana da muhimmanci ga gina ƙasa.” Ya umurci ma’aikata da su yi koyi da al’adun samar da aiki.
“Ƙarshen aiki shi ne yawan aiki. Yawan aiki ne ke kaiwa ga samar da kayayyaki da ayyuka masu gamsarwa da samar da wadata. Don haka ita ce hanyar samun ci gaban ƙasa da kuma ɗaiɗaikun mutane.”
Ministan ya buƙaci ma’aikata da su ƙara ƙaimi wajen bunƙasa sana’arsu ta hanyar da gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke yi na inganta hanyoyin tafiyar da harkokin mulki da kuma sa ka ɗaukacin al’ummar Nijeriya su samu mafi girman moriyar al’umma.
Ministan ya yabawa dukkanin hukumomin tsaro bisa nasarorin da aka samu wajen yaƙar masu aikata laifuka a faɗin ƙasar nan, domin ya ƙara musu ƙwarin gwuiwa da ka da su yi ƙasa a gwiwa wajen daƙile masu aikata laifuka a duk lokacin da suka ɗaga kai.