Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti

0
11
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Laraba 25 ga watan Disamban da muke ciki da Laraba 1 ga watan Janairu mai kamawa a matsayin ranakun domin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya ayyana hakan a madadin gwamnatin tarayyar kasar a sanarwar da babban sakatare a ma’aikatar, Dr. Magdalene Ajani ta fitar, ya miƙa sakon fatan alheri ga ‘yan Najeriya, inda ya buƙacesu da suyi amfani da lokacin hutun domin yin tuntuntuni akan halayen kaunar juna da zaman lafiya da hadin kai da irin wannan lokaci ke koyarwa.

Dr. Tunji-Ojo ya kuma jaddada muhimmancin lokacin a matsayin wanda za’a bunkasa kwanciyar hankali da ƙarfafa zumunta tsakanin iyalai da sauran al’ummar gari.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta ɗaga ranar komawa hutun makarantun firamare da sakandare

Haka kuma ministan ya nemi ‘yan Najeriya su jajirce wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya da haɗin kai da cigaban ƙasa domin samun bunƙasarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here