Gwamnatin Tarayya ta ɗage dokar hana haƙar ma’adinai a Zamfara bayan shekara 5
Gwamnatin tarayya ta ɗage dokar hana haƙar ma’adinai a jihar Zamfara shekara biyar bayan ta kafa dokar.
Ministan Haɓaka Harƙar ma’adinai, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da kuma shafinsa na X ranar Lahadi.
“Gwamnatin Tarayya ta ɗage dokar da ta hana haƙar ma’adinai a jihar Zamfara saboda ƙarin sauƙi da aka samu kan lamarin tsaro a faɗin jihar,” in ji sanarwar da ministan ya fitar.
Alake ya ce Najeriya “za ta ci riba mai yawa idan aka ƙara farfaɗo da harkokin tattalin arziƙi a jiha mai ma’adinai da yawa kamar Zamfara wadda take da zinari da lithium da tagulla da yawa.”
Ministan ya bayyana cewa dokar hana haƙar ma’adinai da aka yi, wadda take da niyya mai kyau, ta bar wani giɓi wanda masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’i’da ba suke amfani da shi wajen satar ma’adinan ƙasa.
Ya jaddada cewa jihar tana da yiwuwar samar wa Najeriya kuɗin shiga mai yawa.
“Barazana ga rayuka da ta sa aka hana haƙar a shekarar 2019 ta ragu. Manyan nasarorin da jami’an tsaro suka samu sun samar da gagarumar raguwa ga rashin tsaro, kuma yanzu da aka ɗage dokar hana haƙar ma’aidinai, sannu a hankali fannin haƙar ma’adinai na Zamfara zai fara ba da nasa gudunmawar ga kuɗin shigar ƙasa,” a cewar Alake.
KU KUMA KARANTA: Najeriya za ta ba da lasisin haƙar maadinai ga kamfanonin da ke aiki cikin ƙasar
“Tun daga farkon gwamnatin Tinubu dai ayyukan jami’a tsaro wadda suke yi bisa bayanan sirri sun yi sanadin kashe manyan ɓarayin daji lamarin da ya rage matsalar tsaro,” in ji ministan.
A ganin Alake, ɗage dokar zai ba da damar sa ido sosai kan harkar haƙar ma’adinai a jihar.
Ya ce wannan zai ba da damar tattara bayanan sirri domin daƙile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba tare da tabbatar da cewa ƙasar ta amfana da arziƙin ma’adinan jihar.
Alake ya jaddada cewa yarjejeniyar da Najeriya ta shiga da Faransa da ya janyo ce-ce-ku-ce kwanakin baya ba ya nufin ƙasar za ta sallamar da ma’adinanta ko kuma ƙulla alaƙar soji da Faransa ba.