Gwamnatin tarayya ta ƙara farashin yin fasfo na tafiye-tafiye

0
78
Gwamnatin tarayya ta ƙara farashin yin fasfo na tafiye-tafiye

Gwamnatin tarayya ta ƙara farashin yin fasfo na tafiye-tafiye

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da ƙarin farashin yin fasfo daga ranar 1 ga Satumba, 2024.

Kakakin Hukumar Kula da shige da fice ta ƙasa (NIS), DCI Kenneth Udo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ƙara da cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da ingancin fasfo ɗin Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu ya ba da umarnin buɗe iyakokin Najeriya da Nijar nan-take

“bisa ƙarin da aka yi, Fasfo mai shafi 32 na shekaru 5 wanda a baya ana cajin Naira Dubu Talatin da Biyar (N35,000.00) zai koma Naira Dubu Hamsin (N50,000.00) kacal; yayin da Fasfo mai shafi 64 mai aiki na shekaru 10 wanda ya kasance Naira Dubu Saba’in (N70,000.00) a baya zai koma Naira Dubu Dari (N100,000.00) kacal.

“Duk da haka, karin bai shafi mazauna kasashen waje ba,” in ji shi.

Leave a Reply