Gwamnatin tarayya bata bamu kuɗin tallafi ba – Gwamnan Oyo
Daga Ali Sanni
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ce sam iƙirarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi, na cewa gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi naira biliyan 570 domin tallafa wa jama’a ba haka bane.
Yayin jawabinsa na kwantar da hankalin al’ummar ƙasar da ke zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta raba kuɗin ga gwamnonin jihohin ƙasar guda 36, domin sauƙaƙa wa al’umma matsin rayuwa.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta bai wa masu ƙananan sana’o’i tallafin 600,000 sannan kuma akwai wasu ƙarin ƙananan sana’o’in 400,000 daza su amfana da tallafin su ma.
Sai dai cikin wani dogon saƙo da Gwamnan na Oyo ya sanya a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya ce shi dai jiharsa bata san da wannan kuɗi da Tinubun ya ce gwamnatinsa ta raba wa jihohi ba.
Gwamnan ya ce yana mayar da martani ne kan maganar da wani ɗan jiharsa yayi kan iƙirarin Gwamnatin Tarayyar cewa ta raba wa jihohi sama da naira biliyan 570 domin tallafa wa al’umma kan ƙuncin rayuwa.
KU KUMA KARANTA;Sanata Ndume ya gana da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa
A cewar Makinde, “maganar na daga irin batutuwan da Gwamnatin Tarayyar ke yi ne na faɗin abin da ba haka yake ba.
“Kuɗaden da ake magana na daga cikin rancen Bankin Duniya na shirin NG-CARES, wanda kuɗi ne da ake tallafa wa jihohi wajen farfaɗowa daga annobar Korona, inda jiha za ta yi amfani da kuɗinta ta aiwatar da shirin, daga baya kuma Bankin Duniya ya mayar mata da kuɗin ta hanyar Gwamnatin Tarayya bayan bankin ya tantance abubuwan da jihar ta yi da nasarorin da ta samu.
“Ya kamata mufa sani cewa kuɗin na bankin Duniya bashi ne ga jihohi ba tallafi ba, saboda haka jihohi za su biya kuɗin.
Gwamnan ya ce jiharsa ta samu kuɗin kashi biyu, inda a kashin farko aka ba ta naira biliyan 5.98, sannan a kashi na biyu ta samu naira biliyan 822.
“Saboda haka a taƙaice gwamnatin tarayya ba ta ba jihar Oyo wani kuɗi ba.
Makinde shi ne gwamnan jam’iyyar PDP, na biyu da ya soki Tinubu a kan jawabin a kwanakin nan.
Ana iya tuna cewa a baya-bayan nan ne Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce jawabin shugaban soki-burutsu ne kawai kuma fanko ne da babu abin ɗauka a cikinsa.