Gwamnatin Senegal ta rufe dukkan sansanin sojin Faransa da ke ƙasar

0
31
Gwamnatin Senegal ta rufe dukkan sansanin sojin Faransa da ke ƙasar

Gwamnatin Senegal ta rufe dukkan sansanin sojin Faransa da ke ƙasar

Gwamnatin Senegal ta sanar da rufe dukkan sansanonin sojin Faransa da ke cikin ƙasar.

Wannan mataki ya zo ne a matsayin wani yunkuri na tabbatar da cikakken iko kai da kai na ƙasar, tare da nuna sabon alkiblar manufofin diflomasiyya da tsaro.

A cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce wannan shawarar an yanke ta ne domin sake fasalta dangantakar tsaro tsakanin ƙasar da Faransa, da kuma kare muradun ƙasa. Sai dai ba a bayyana lokacin da matakin zai fara aiki ba.

KU KUMA KARANTA:Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji sama da 200 ya kife cikin ruwa a Neja

Tun da farko dai, wasu ƙasashen yammacin Afirka sun dauki irin wannan matakin, musamman a sakamakon ƙorafe-ƙorafen jama’a kan rawar da sojojin Faransa ke takawa a harkar tsaro a yankin Sahel.

Masu nazarin al’amuran siyasa na ganin wannan matakin na iya kara tsaurara dangantaka tsakanin Senegal da Faransa, wadda ta kasance tsohuwar ƙasar mulkin mallaka.

Leave a Reply