Gwamnatin Sakkwato za ta binciki harin jirgin Soja da ya kashe mutane 10
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce za ta haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin bincikar dalilin harin jirgin saman yaƙi da aka kai wasu ƙauyukan jihar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10.
Harin ya faru ne lokacin da jirgin yakin ya kai farmaki a sansanonin ’yan ta’adda na Lakurawa, waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a jihar.
Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya tabbatar da mutuwar mutane a sakamakon harin jirgin yaƙi a ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar hukumar Silame.
Ya ce harin ya faru ne bisa kuskure.
Ba wannan ne karo na farko ba da ake samun kuskuren irin wannan farmaki ba.
KU KUMA KARANTA: Najeriya ta tabbatar mutum 85 sojoji suka kashe bisa kuskure a Kaduna
A watan Disamban 2023, irin haka ya faru a Tudun Biri, a Jihar Kaduna, haka kuma ya taɓa faruwa a jihohin Nasarawa da Adamawa.
’Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa, inda ƙungiyar tuntuɓa ta arewa ta buƙaci a ɗauki matakin kare faruwar irin wannan kuskure a nan gaba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin, Lt. Col. Abubakar Abdullahi, ya ce sojojin suna aiki ne bisa bayanan sirri da suka samu.
Sai dai, ya nuna rashin jin dadi kan yadda ake yada labaran da ba su da tabbaci a kafafen sada zumunta.
A halin yanzu, mutanen ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa na cikin alhini kan mutuwar mutane 10, tare da fargabar abin da ka iya sake faruwa.