Gwamnatin Nijar ta amince da tattaunawa don gyara alaƙa da Jamhuriyar Benin
Hukumomin ƙasashen biyu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters a ranar Laraba cewa ba a yanke ranar da za a gudanar da taron ba.
Tiani ya shaida wa tsofaffin shugabannin kasar ta Benin cewa, a shirye yake don tattaunawa ta gaskiya.
Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta amince da tattaunawa da gwamnatin Jamhuriyar Benin karkashin jagorancin tsofaffin shugabannin kasar Benin guda biyu, domin taimakawa wajen maido da dangantaka bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a bara wanda ya kai ga rufe kan iyaka da kuma rufe wani bututun mai da China ke mara wa baya.
Nijar ta amince da tattaunawar ne bayan wata ganawa da shugabanta na soji Janar Abdourahamane Tiani da tsofaffin shugabannin kasar Benin Thomas Boni Yayi da Nicephore Soglo suka yi a ranar 24 ga watan Yuni, wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata da marece ta fada.
Hukumomin ƙasashen biyu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters a ranar Laraba cewa ba a yanke ranar da za a gudanar da taron ba.
KU KUMA KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta nemi Nijar ta kama shugaban ‘yan bindiga da take nema
Wani ƙuduri zai iya ba da damar sake dawo da tura man da ke kwarara zuwa kasar Sin ta bututun mai da PetroChina ke mara wa baya.
Nijar ta dakatar da fitar da mai ta bututun mai tsawon kilomita 2,000 zuwa gaɓar Tekun Benin a tsakiyar watan Yuni yayin da ake ta takun-saƙa game da rufe iyakokin.
Rikicin dai ya samo asali ne tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a watan Yulin 2023, wanda ya sa Ƙungiyar Hadin Kan Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi fiye da watanni shida.
Tun daga lokacin ne dangantaka ta yi tsami tsakanin Nijar da makwabtanta, inda Nijar ta zargi kasar Benin da karbar bakuncin ‘yan tada kayar baya da ke yunkurin kawo rudani a yankin Sahel. Benin dai ta musanta zargin.
Wata kungiyar ‘yan tawayen Nijar da ke adawa da gwamnatin mulkin soji ta yi wa bututan zagon kasa a watan Yuni, wanda ya haifar da ‘yar ƙaramar ɓarna.
Tiani ya shaida wa tsofaffin shugabannin kasar ta Benin cewa, a shirye yake don tattaunawa ta gaskiya, kuma ya amince da wata shawara daga gare su na kwantar da tarzoma, a cewar sanarwar.
Sanarwa ta ce “Ya amince da ƙa’idar kafa kwamitin da ya ƙunshi wakilai daga gwamnatin Nijar, gwamnatin Benin da kuma tsofaffin shugabannin kasar Benin biyu da suka kai ziyara.”
Tsofaffin shugabannin sun yi wata ganawa ta gaba da shugaban kasar Benin, Patrice Talon a ranar Litinin, in ji wata sanarwa ta daban.
“Shugaban kasa da tsofaffin shugabannin kasar sun amince da bukatar sake fara tattaunawa kamar yadda dukkan bangarorin suka amince da su,” in ji ta.