Gwamnatin tarayya ta naɗa Farfesa Mahmud Raji a matsayin sabon babban daraktan kula da lafiya na Asibitin ƙasa dake Abuja, (National Hospital Abuja).
Mista Raji shi ne likitan da ya ceci rayuwar Yusuf Buhari a hatsarin da ya yi a Abuja a shekarar 2017.
A wata sanarwa da Asibitin ya fitar ranar Juma’a a Abuja, ya ce Mista Mahmud ya karɓi takardar naɗin nasa daga ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire.
A cewar sanarwar, Mahmud, wanda yanzu shi ne babban jami’in gudanarwa, na babban jami’in Asibitin, Farfesa ne a fannin aikin jinya. Ƙwararren likita ne, wanda ya kafa sashen aikin tiyatar jijiya na Asibitin ƙasa a shekarar 2010.
KU KUMA KARANTA: Wasu jihohi a arewacin Najeriya za su fuskaci ƙarancin ruwan sama – NEMA
Sabon CMD ya karɓi lambobin yabo da yawa da karramawa a cikin gida da na duniya.
Ya horar da likitocin neurosurgeons fiye da 30, ya ba da surori 10 a cikin littattafan neurosurgical kuma ya buga labarai sama da 50 a cikin mujallun da aka yi bita a duniya.
[…] Source link […]
[…] KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta naɗa Farfesa Mahmud shugaban asibitin ƙasa da ke Abuja […]