Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun ƙaramar sallah

0
216
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun ƙaramar sallah

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun ƙaramar sallah

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu.

KU KUMA KARANTA:Majalisar wakilai a Najeriya, ta amince da ƙudirin dokar haraji a ƙasar

A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya.

Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.

Leave a Reply