Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yunin 2023 a matsayin hutun babbar Sallah (Eid-El-Kabir).
Sanarwar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida Oluwatoyin Akinlade ya fitar.
“Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Laraba, 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni 2023 a matsayin ranakun hutun jama’a domin tunawa da bikin Eid-el-Kabir na wannan shekara tare da taya al’ummar musulmi barka da Sallah a gida da kuma ƙasashen waje,” in ji sanarwar.
KU KUMA KARANTA: Akwai yiwuwar akai hare-hare a lokacin bukukuwan Sallah – SSS
Mista Akinlade ya yi ƙira ga Musulmai da dukkan ‘yan Najeriya da su yi wannan sadaukarwa domin ci gaban al’ummarmu da kuma ci gaban ƙasarmu Nijeriya.
Sakataren dindindin ya bayyana fatan cewa addu’o’i da sadaukarwar da aka yi a bana za su dawo da zaman lafiya da haɗin kai da ake so a ƙasar nan.
“Muna fatan addu’o’i da sadaukarwa da aka yi tare da wannan gagarumin biki, da kuma saƙon Eid-ei-Kabir, za su samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Najeriya,” in ji sanarwar.
[…] KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta ayyana laraba da alhamis a matsayin ranakun hutun babbar Sallah […]