Gwamnatin Kano ta yi watsi da ƙudurorin dokar haraji

0
16
Gwamnatin Kano ta yi watsi da ƙudurorin dokar haraji

Gwamnatin Kano ta yi watsi da ƙudurorin dokar haraji

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da ƙudurorin dokar haraji da ake ta cece-kuce a kan shi tsawon watanni a Najeriya.

Gwamnatin, ta bakin mataimakin gwamnan, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a wajen bikin sabuwar shekara da ya gudana a filin Mahaha a Kano, ta baiyana matsayin ta cewa ba ta tare da waɗannan ƙudurorin.

KU KUMA KARANTA: An dakatar da sabuwar dokar haraji a Najeriya

A wata sanarwa da kakakin mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu ya fitar, Gwarzo ya ce ƙudurorin dokar haraji ba shi ne mafita a halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasar.

Gwarzo ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba ta goyon bayan ƙudirorin, inda ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa juriya da haƙuri da halin ƙunci rayuwa da ake fama da shi a ƙasar.

Leave a Reply