Gwamnatin Kano ta tabbatar da ɓullar cutar mashako a jihar

2
435

Daga Shafaatu Dauda,Kano

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da ɓullar cutar da ke sarƙafe numfashi ta diphtheria a ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Wannan na zuwa ne sa’o’i 48 bayan rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, inda ya bayyana bullar cutar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 25 kamar yadda ya faru a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa kan ɓullar cutar zazzaɓin Diphtheria da Lassa a jihar.

Ya ce an samu mutane 100 da ake zargin sun kamu da cutar inda uku suka mutu.

KU KUMA KARANTA:Ansamu masu cutar Ƙyandar-Biri a jihar Borno

“Ya zuwa ranar 20 ga watan Janairun 2023 mun sami rahoton bullar cutar guda 100 da ake zargi daga ƙananan hukumomi 13.

“Ƙananan hukumomin sun haɗar da Ungogo, Nassarawa, Bichi, Dala, Dawakin Tofa, Dawakin Kudu, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Ƙiru, Rano, da kuma Gwarzo”. in ji shi.

Dr Tsanyawa ya ce a halin yanzu majiyyata 27 suna karɓar magani yayin da 41 kuma aka sallame su.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, a ranar 10 ga watan Janairu, cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kiwon lafiyar ta samu rahoton da ake zargin mutanen sun kamu da cutar zazzabin Lassa a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da ke Kano.

Ya ce an tura wata tawaga domin gudanar da bincike, an ɗauki samfurin gwajin a ɗakin gwaje-gwaje sannan bayan kwana uku sakamakon ya nuna sun kamu da zazzaɓin Lassa.

“An ɗauki samfura 10 daga cikin mutanen da ke da hatsarin kamuwa da cutar, 3 sun kamu da cutar, wanda adadin ya kai 4 waɗanda a halin yanzu ake kulawa da su a asibitin koyarwa na Aminu Kano,” in ji Tsanyawa.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da cibiyar killace masu cutar ta Kwanar Dawaki domin killace masu cutar zazzaɓin Lassa.

Ya ƙara da cewa an horar da ma’aikatan lafiya tare da tura su cibiyar keɓewa inda kuma yayi nuni da cewa jihar za ta gudanar da aikin rigakafi na yau da kullun ga kananan hukumomin da abin ya shafa.

2 COMMENTS

Leave a Reply