Gwamnatin Kano ta mayar da martani kan ɗaga tuta a fadar Nasarawa
Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da batun ɗaga tutar masarauta da aka yi a gidan sarki na Nassarawa wurin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ke zaune, inda ta bayyana hakan da ƙoƙarin jan hankalin jama’a kawai.
Tutar, wata alama ce ta iko dake nuni da cewar Sarki na nan, a kullum ana ɗaga ta da misalin ƙarfe 6 na safe a kuma sauƙe ta da misalin ƙarfe 6 na yamma. Duk lokacin da sarki ba ya cikin fada ko ya yi balaguro za ta kasance a sauƙe.
Da safiyar ranar Alhamis, aka lura cewar an ɗaga tutar da misalin ƙarfe 6 na safiya a fadar Nassarawa, abin da ya haifar da kace-nace dama raɗe-raɗi.
Kowane daga cikin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II na iƙirarin shi ne Sarkin Kano kuma suna ci gaba da aiwatar da ayyukan sarauta.
KU KUMA KARANTA:An sauya Kwamishinan ’yan sandan Kano
Gwamnatin jihar ce ta sauƙe Aminu Ado Bayero tare da sake naɗa Muhammadu Sanusi biyo bayan yiwa dokar masarautu ta Kano kwaskwarima.
An ɗaga irin wannan tuta a fadar gidan Rumfa, inda Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ke zaune.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya yi fatali da batun ɗaga tuta a fadar Nassarawar, inda yace hakan wani yunƙuri ne na jan hankalin al’umma.
Ya shaidawa manema labarai cewar, “hakan wani yunƙuri ne na jan hankalin al’umma. Amma babu shakku ko tantamar cewar Sanusi ne Sarkin Kano.