Gwamnatin Kano ta maka mawaƙi Rarara a kotu

0
26
Gwamnatin Kano ta maka mawaƙi Rarara a kotu

Gwamnatin Kano ta maka mawaƙi Rarara a kotu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta kai mawaƙin siyasa Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ƙara a kotu bisa sakin wata waƙa da hukumar ta ce bai kawo ta tantance ta ba.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya aikawa da manema labarai, hukumar ta ce tun tuni ta aika wa da mawaƙin saƙon ƙorafi dangane da sabuwar waƙar da ya saki ba tare da ya kawo an tace ba, amma ya ƙi ba ta amsa.

A cewar sanarwar, hakan ne ya sa hukumar ta garzaya gaban kotun.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa tuni kotun ta aika wa da mawaƙin takardar sammaci sai dai ba a ga fuskarsa ba a yau 13 ga watan Nuwamba a yayin zaman kotun.

KU KUMA KARANTA: Ma mallakin shafin Facebook ya cire shafin mawaƙi Rarara

Tun kafin wannan lokacin bayan sakin sabuwar waƙar Hukumar tace fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta turawa mawaƙin saƙon neman ba’asi ta hanyar saƙon karta kwana, sai de har kawo ya wannan lokaci mawaƙin bai ba wa hukumar amsar saƙon ba.

Leave a Reply