Gwamnatin Kano ta karɓo bashi daga Faransa domin aikin ruwan sha

0
58
Gwamnatin Kano ta karɓo bashi daga Faransa domin aikin ruwan sha

Gwamnatin Kano ta karɓo bashi daga Faransa domin aikin ruwan sha

Gwamnatin Jihar Kano ta samu rancen Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Raya kasar Faransa gina sabbin matatun ruwa a Tamburawa da inganta samar da ruwan sha.

Gwamna Abba ya ce aikin na da nufin inganta hanyoyin samun ruwan sha, duba da karuwar al’ummar jihar cikin hanzari.

Abba ya jaddada mahimmancin aikin, wanda ya ce fuskanci tsaiko sakamakon annobar COVID-19 da sauran kalubale, amma yanzu ana sa ran kammala shi nan da shekaru biyu masu zuwa.

Ya ce za a gudanar da aikin ne a karkashin shirin sake fasalin ruwan birane na kasa, kuma ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya ta ba da tabbacin hakan.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Ali Haruna Makoda, yayin wani taron bitar ayyuka na kwanaki biyu da aka gudanar a Kano, wanda ya samu halartar wakilai daga jihohin Filato, Enugu, da Ondo.

KU KUMA KARANTA: Ƙarin farashin man fetur ya karya darajar mafi ƙarancin albashi na dubu 70 — NLC

Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, Garba Ahmad Bichi, ya bayyana cewa, aikin ya hada da gina sabuwar ma’ajiyar ruwa mai daukar lita miliyan 250 a kowace rana, wanda zai magance matsalar karancin ruwan da ake fama da ita a cikin birnin, sakamakon karuwar al’umma.

Leave a Reply