Gwamnatin Kano ta buƙaci Tinubu da ya ɗauke Sarki Aminu Ado daga jihar

0
21
Gwamnatin Kano ta buƙaci Tinubu da ya ɗauke Sarki Aminu Ado daga jihar

 

Gwamnatin Kano ta buƙaci Tinubu da ya ɗauke Sarki Aminu Ado daga jihar

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin jihar kano ta bukaci Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya dauke Sarki Aminu Ado Bayaro daga jihar kano domin samarwa da jihar masalaha, la’akari da yadda wasu ke amfani da wannan damar wajen neman tayar da husuma a jihar.

Mataimakin gwamnan kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, shine ya bayyana hakan, Jim kadan bayan rabon tallafin babura da kudi da keken dinki wanda dan majalissar dokokin Mai wakilintar karamar hukumar Tarauni Kabiru Dahiru sule ya raba ga Al,ummar karamar hukumar Tarauni.

Inda yace zaunar da sarkin kano na sha biyar a gidan sarkin na Nassarawa anyi shi da wata niya domin hana gwamnatin kano ta zauna lafiya da kuma kin yiwa al’ummar jihar abin da ya dace.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya lashe lambar yabo ta gwamna mafi ƙwazo a Afirka

Haka zalika Aminu Abdussalam Gwarzo yace zanga-zanga da al’umma suka fito a wannan satin, al’umma suna da hakkin fitowa domin nuna goyon bayan su kan abin da suke so, da suke bukatar a cire sarkin kano na sha biyar daga gidan Nasarawa amma aka turo jami’an tsaro suka hana su tare da kama wasu daga ciki.

Mataimakin Gwamna Gwarzo ya kuma ce suna kira ga shugaban kasa da ya gaggauta dauke sarki Aminu daga cikin jihar Kano domin barin al’umma su zauna lafıya.

Yakara da cewa Gwamnatin kano ta ce yadda doka ta kawo tsohon sarkin haka doka ce ta kawo sabon Sarkin don haka abar doka tayi aikinta.

Leave a Reply