Gwamnatin Kano ta ba da umarnin cafke ‘yan jarida 2 kan wallafa wani rubutu

0
259
Gwamnatin Kano ta ba da umarnin cafke 'yan jarida 2 kan wallafa wani rubutu

Gwamnatin Kano ta ba da umarnin cafke ‘yan jarida 2 kan wallafa wani rubutu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Waya, ya bayar da umarnin tsare wasu ‘yan jarida guda biyu—Buhari Abba, Mawallafi kuma Manajan Editan Kano Times, da Isma’il Awwal, ɗan jaridar Sahelian Times, kan wani ra’ayi da aka buga a kafafen yaɗa labarai da dama a ranar 24 ga Fabarairu, 2025. Ra’ayin mai taken “Mai girma Gwamna Abba Kabir, Hattara ta Waiya” an rubuta shi ne cikin harshen turanci.

Rahotanni sun ce Kwamishinan ya yi amfani da jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta jihar Kano (SCID) wajen kamawa tare da tsare ‘yan jaridar biyu.

Kamar yadda jaridar Daily Struggle ta ruwaito, ‘yan sanda sun fara gayyatar ‘yan jaridar ne a ranar Asabar 22 ga watan Maris, 2025. An tsare su ne a ranar Litinin, 24 ga watan Maris, lokacin da aka ɗauki bayanansu kafin a bayar da belinsu, tare da umurtar su da su dawo da safen washegari.

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan sanda sun tursasa Buhari Abba ya bayyana sunan marubucin da kuma adireshinsa.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya ba wa marayu biyu kujerun aikin Hajji

A martanin da suka mayar, da yawa daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta sun ƙaddamar da kamfen na ganin an sako ‘yan jaridar, inda suka yi amfani da maudu’in #FreeBuhari da kuma #FreeIsmail, inda suka buƙaci hukumomi da su mutunta ‘yancin ‘yan jarida da kuma daina danne kafafen yaɗa labarai.

Ƙungiyar ‘yan jaridar yanar gizo ta Kano (ASKOJ) ta yi Allah-wadai da tuhumar da ake yi wa memban ƙungiyar, Buhari Abba.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar ASKOJ Yakubu Salisu ya sanyawa hannu kuma ya fitar a ranar Talata, ƙungiyar ta buƙaci a dakatar da daƙile ‘yancin ‘yan jarida da kuma duk wani yunƙuri na amfani da jami’an tsaro kan ‘yan jarida.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Dole ne cibiyoyin tsaro su kiyaye doka kuma su yi watsi da amfani da su wajen aikata zalunci.”

Leave a Reply