Gwamnatin Jigawa za ta ƙaddamar da shirin bunƙasa ilimi a faɗin jihar – Dakta Hauwa M. Ɓaɓura
Daga Abubakar M. Taheer
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta fara gudanar da shirin ‘Citizen Leads Initiative’ nan ba da daɗewa ba domin bunƙasa harkokin ilimi da koyarwa a jihar.
Hakan na tafe ne cikin wata zantawa da ƙwararriyar mai bawa Gwamna shawara kan harkokin Ilimi, Dakta Hauwa Mustapha Ɓaɓura ta jihar Jigawa, kan halin da jihar take ciki na taɓarɓarewar harkokin ilimi wanda Gwamnatin jihar za ta gayyaci sarakuna, ‘yan kasuwa, Malamai da masu riƙe da madafun iko domin ciyar da farfaɗo da ilimin ‘ya’yan jihar.
Shirin ‘Citizen Leads initiative’ zai kasance wata hanya ta musamman da dukkan ɓangarorin al’ummar daga ciki da wajen jihar za su haɗu domin saka ido, gudanar da bita ga malaman makarantu, ɗalibai, dama tarukan wayar da kai ga al’ummar dake faɗin jihar ta Jigawa.
Dakta Ɓaɓura ta ƙara da cewa ya zama haƙƙi da Allah ya ɗora mana gaba ɗayanmu ‘yan jihar Jigawa damu sauƙe nauyin ilimantar da ‘ya’yanmu, jikokinmu dana ‘yan’uwanmu.
Ba dole sai Gwamnati ce kaɗai ke da wannan nauyi a kanta ba.
Akwai abun takaici al’umma suna gani wasu ɓata-gari su rinƙa ɓarnata kadarorin makarantunmu suna sacewa mu kuma zuba musu ido, wannan babbar illa zai mana ga goben yaranmu.
KU KUMA KARANTA: Za a fara amfani da sabuwar manhajar ilimi a watan Janairun – Ministan Ilimi
Dole sauran al’umma su kula da Makarantu, kula da inganci ilimin, saka ido wajen zuwan malamai makarantu, ta haka ne zamu taro saura jihohi da ake alfahari dasu wajen ci gaban ilimi a ƙasar nan.
A ƙarshen Dakta Hauwa Mustapha Ɓaɓura ta ƙara da cewa Gwamnatin Jihar a shirye take wajen karɓar shawara daga masana, ƙungiyoyi dama gudanar da bita ga Malamai, ɗalibai dama dukkan sauran al’ummar jihar ta Jigawa.
A cikin satin da ya gabata gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya ware kuɗi Naira Miliyan 740 domin gina ajujuwa, ɗakunan gwaja-gwaje, banɗakai a wasu makarantun jihar tare da ɗaukan matakin mayar da yaran dake gararanba a tituna zuwa makaranta.
Alƙaluma daga Hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar Jigawa (UBEC) sun nuna cewa kusan yara 400,000 ne basa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sa take cikin na gaba-gaba a faɗin ƙasar nan.
Ko a shekarar 2022 hukumar kula da asusun kula da ilimin yara na Majalissar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa yara 700,000 ne a jihar ta Jigawa basa zuwa makaranta.