Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Akpabio ya bayyana cewa Tinubu yana ƙoƙarin gyara tattalin arziƙin ƙasar nan ne wanda ya zargi Gwamnatin Bahari da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, tayi masa babban giɓi.
Tattalin arziƙi ya taɓarɓare Akpabio ya yi nuni da cewa Shugaba Tinubu ya gaji tattalin arziƙi ne wanda ya kusa durƙushewa inda yanzu yake ƙoƙarin yin amfani da basirarsa wajen ceto shi, cewar rahoton jaridar Leadership.
KU KUMA KARANTA: Ministocin Tinubu ne suka sa ba a ganin ƙoƙarinsa – Sanata Jimoh
Shugaban majalisar dattawan shima wanda EFCC ke Zargin sa da da sace kuɗaɗen jiharsa ya yi wannan roƙon ne a filin wasa na Ikot Ekpene da ke jihar Akwa Ibom a ƙarshen mako a wajen wata liyafa da aka shirya masa tun bayan zamansa shugaban majalisar.
Ya bayyana cewa yana kan bakansa na cewa Emefiele ne babban mai laifi kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki duk kuwa da ƙarar da tsohon gwamnan na CBN ya kai shi kotu saboda cewa hakan.
Tinubu zai gyara tatttalin arziƙi Ya nuna ƙwarin gwiwarsa cewa Tinubu zai dawo da tattalin arziƙin ƙasar nan kan turba kamar yadda ya yi a jihar Legas lokacin da ya riƙe muƙamin gwamna