Gwamnatin Borno ta gabatar da ƙa’idojin sanya tufafi ga ‘yan matan sakandare

0
313

Gwamnatin jihar Borno ta ɓullo da tsarin sanya tufafin dole ga ɗalibai musulmi mata a dukkan makarantun sakandaren gwamnati.

Sabuwar dokar saka kayan za ta fara aiki daga zangon karatu na farkon shekarar 2023/2024.

Daraktan kula da makarantu na ma’aikatar ilimi ta jihar Borno, Bukar Mustapha-Umara ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Alhamis.

Ya ce a ƙarƙashin tsarin saka kayan, dole ne kowane ɗalibi ya sanya wando, rigar kwata, ɗankwali da himar ( mayafi) a makaranta.

KU KUMA KARANTA: Jami’ar ATBU ta hana shigar nuna tsaraici ga ɗalibai

Daraktan ya ce dole ne dukkan shugabannin makarantun sakandire su tabbatar da bin ƙa’idojin sabuwar shigar. “Wannan shigar ta zama wajibi ga dukkan ɗalibai mata musulmi a duk makarantunmu na sakandire da ke jihar.

“Amma ga ɗalibai Kirista mata, zaɓi ne. Za su iya kasancewa da shigar da suke da ita a yanzu ko kuma su canza wando,” in ji Mustapha -Umara.

Ya yi ƙira ga iyaye da ’yan uwa da su yi tanadin isassun shirye-shirye na sabon shigar makaranta kafin a fara wani sashin karatu na 2023/2024.

Leave a Reply