Gwamnatin jihar Borno za ta ba da tallafin karatu na musamman ga ɗalibai marasa galihu da ke karatun aikin jinya da ungozoma.
Sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar, Bala Isa ne ya bayyana haka a Maiduguri ranar Juma’a.
“Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, na bayar da tallafin karatu na musamman ga ‘yan asalin jihar Borno masu sha’awar karatun aikin jinya da ungozoma.
Ɗaliban dole ne su sami maki a Turanci, Liffafi, Biology, Chemistry da Physics a cikin WAEC, NECO ko NABTEB.
KU KUMA KARANTA: Gidauniyar ba da zakka a Legas ta ba da tallafin karatu ga marayu 22 a Zamfara
Isa ya ce duk masu sha’awar su miƙa takardar shaidarsu ga hukumar bayar da tallafin karatu kafin ranar 2 ga watan Agusta.
Gwamna Zulum ya yi jawabin buɗe wa’adin zango na biyu, ya bayyana shirin gina ƙarin makarantar koyon aikin jinya da ungozoma guda biyu a jihar domin samar da ƙarin ma’aikata ga ɓangaren lafiya.