Gwamnati zata haɗa kai da masu maganin gargajiya don magance matsalolin kisan kai da ƙungiyoyin asiri ke yi a Ogun

0
491

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya nemi haɗin kan gwamnatin jihar da masu maganin gargajiya domin kawo ƙarshen kashe kashe da ‘yan ƙungiyoyin Asiri ke yi a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar talata yayin da yake jawabi a taron bita na kwana ɗaya, kan yunƙurin da ake yi na yaƙi da kashe-kashe da tashe-tashen hankula da nufin inganta magungunan gargajiya don kare lafiyar kowa.

Hukumar magungunan gargajiya ta musamman (Alternate Medicine) reshen jihar Ogun tare da haɗin gwiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun ne suka shirya taron a Abeokuta.

Gwamna Dapo Abiodun wanda ya yi Allah wadai da munanan ayyuka na masu kashe kashe na al’ada ko tsafi na ƙungiyoyin asiri da kuma irin munanan kalamai da ake yi musu, musamman a Jihar Ogun, ya ce dole ne kowa ya tashi tsaye don fallasa masu hannu a wannan aika-aika domin kawo ƙarshen wannan matsala, “domin tona asirin waɗanda ke cikinku masu ɓata sunanku da kyawawan ayyukan, dole ne ku ware kanku daga kashe-kashen al’ada kuma ku ci gaba da zama mutane na gari.”

KU KUMA KARANTA:An gano wajen da ake sayar da jarirai kan kuɗi N400,000 a Ogun

Ya kuma yaba wa ƙwararrun da suke bayar da gudunmawa wajen samar da kiwon lafiya ga jama’a, musamman waɗanda ke yankunan karkara, yana mai ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sun sami isassun horo don samar da ingantaccen kiwon lafiya.

Ya ce magungunan gargajiya sun daɗe ana yin su, kuma sun kasance masu amfani ga al’umma a baya, inda ya jaddada bukatar ƙwararrun, su yi amfani da hanyar kimiyya wajen samar da kayayyakinsu, inda ya ce ya zama wajibi hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki su dinga gwadab kayayyakin da ake samarwa na maganin gargajiya domin tabbatar da su da kyau don amfanin ɗan adam.

A cewar gwamnan, “Lokaci ya yi da za a sa magungunan Afirka su zama masu fa’ida ta hanyar bincike na kimiyya da kyawawan ayyuka.

“Hakan zai sa magungunan su yi gogayya da takwarorinsu a fagen duniya da kuma inganta lafiyar jama’a.” Inji shi.

A ƙarshe gwamnan ya yabawa ma’aikatan da suka himmatu wajen koyo da kuma inganta kansu, inda ya ba da tabbacin cewa za a ba su fili su gina ofishinsu, yayin da gwamnati za ta samar da motar bas domin sauƙaƙa masu zirga-zirga.

A nata jawabin kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dokta Tomi Coker, ta ce gwamnati mai ci a jihar za ta ci gaba da bayar da gudunmawarta wajen ganin an ƙayyade wasu magunguna na daban, domin tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar jihar.

Coker wanda ta ci gaba da nuna cewa al’amarin kashe-kashe na al’ada na daukar mataki mai haɗari a jihar, ta bayyana cewa, kawo yanzu gwamnatin jihar ta yi rijistar mata masu kula haihuwa na gargajiya sama da 1,000, inda ta yi ƙira da a madadin masu ba da magunguna su zama jakadun jihar ta hanyar yaƙi da kashe-kashen al’ada da a tsakanin su.

A jawabinsa na maraba, shugaban hukumar magungunan gargajiya reshen Jihar Ogun, Nurudeen Olaleye, ya ce hukumar da ke k’ƙarkashin sa, ta sa ido a kan ayyukan likitocin a jihar.

Olaleye ya kuma ƙara da cewa, sakamakon binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa wadanda ke da hannu a ayyukan ba bisa ka’ida ba a jihar ba su da rajista, yana mai jaddada cewa tawagar da ke sa ido za ta ci gaba da gudanar da atisayen sa ido domin daƙile ayyukan baragurbi a cikin sana’ar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun Lanre Bankole, wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Mista Babatunde Sodimu ya wakilta, ya buƙaci masu maganin gargajiya da su rubuta tsarinsu tare da ƙara yin bincike don inganta ayyukansu.

Bankole ya kuma bayyana cewa ya kamata yayi ma’aikatan su ƙara kwarin gwiwa da ɗaukar nauyin ƙudirin da zai taimaka wajen bunkasa ayyukansu, ya ce rundunar ‘yan sandan jihar tana fahimtar mahimmancin su kuma a shirye take ta tallafa musu a kowane lokaci.

Leave a Reply