Gwamnan Yobe ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin Tafkin Chadi
Daga Ibraheem El-Tafseer
An yau juma’a da aka shiga kwana na uku a taron gwamnonin tafkin Chadi da ke ci gaba da gudana a birnin Maidugurin jihar Borno, inda aka tattauna kan illar shan muggan ƙwayoyi da safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin yankin tafkin Chadi.
Bayan kammala zaman ne aka naɗa Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban ƙungiyar gwamnonin tafkin Chadi na tsawon shekaru 2 masu zuwa.
KU KUMA KARANTA:Mataimakin shugaban Najeriya ya buɗe taron gwamnonin yankin tafkin Chadi
Gwamnan ya karanta jawabin karɓar shugabancin nasa, sannan Gwamnan Diffa, Birgediya Janar Mohammadou Ibrahim Bagadoma ya karanta sanarwar da aka har haɗa a ƙarshen taron.