Gwamnan Yobe ya amince da ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

0
18
Gwamnan Yobe ya amince da ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan Yobe ya amince da ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da Naira 70,000 matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikatan jihar, wanda zai fara aiki daga watan Disamban 2024.

Wannan ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya bayar kan sabon tsarin albashin.

Kwamitin ya kuma bayar da shawarar gyara yadda ake raba kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar, domin tabbatar da cewa sabon tsarin albashin ya fara aiki a dukkanin ƙananan hukumomin jihar.

Ana sa ran kammala shirye-shiryen da ake yi nan ba da jimawa ba, don tabbatar da cewa ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar su ma sun fara samun sabon albashin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Ekiti ya amince da biyan ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnatin jihar ta buƙaci ma’aikata su ƙara dagewa wajen yin ayyukansu, domin nuna godiyarsu ta hanyar inganta ayyukan da aka ɗora musu.

Leave a Reply