Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya saka hannu kan wata sabuwar doka wadda ta haramta wa jama’a ɓoye kayan abinci a jihar.
Dokar ta haramta ɓoye duk wani nau’in tsaba da hatsi waɗanda suka haɗa da shinkafa da masara da gero da dawa da waken suya da gyaɗa da sauransu.
Dokar ta tanadi cewa duk mutumin da aka kama ko kamfani yana ɓoye kayan abinci za a gurfanar da shi a gaban kotu domin yi masa hukunci, kan saɓa wa sashe na 114 na kundin laifuka na penal code.
Sannan dokar ta tanadi cewa shi kansa rumbun da aka kama aka kuma tabbatar da cewa ana boye wadannan kayan abinci, za a fasa shi a fitar da abincin don sayar wa al’umma a farashin da ya dace.
KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro su ɗauki duk matakin da ya dace kan masu ɓoye kayan abinci – Tinubu
Haka kuma ya kafa wani kwamiti na musamman da za a ɗora wa alhakin bi lungu da sako na jihar domin zaƙulo mutanen da suke boye kayan abinci.
Gwamnan ya ce kwamitin wanda zai kunshi shugaba da aƙalla mambobi goma daga faɗin jihar, zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da masu ruwa da tsaki a jihar da jami’an tsaro domin ganowa da kuma kama masu ɓoye abinci da gurfanar da su a gaban kotu.
Haka kuma kwamitin zai rinƙa sa ido kan yadda ake sayar da abinci da jigilarsa.
Dokar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da shawara ga gwamnonin ƙasar kan suyi koyi da Jihar Kano wurin yaƙi da masu ɓoye abinci.