Gwamnan Kano ya ɗauki masu gadi 1,600 aiki don kula da tsaron makarantu a Kano

0
162
Gwamnan Kano ya ɗauki masu gadi 1,600 aiki don kula da tsaron makarantu a Kano
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Kano ya ɗauki masu gadi 1,600 aiki don kula da tsaron makarantu a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da tura sababbin ma’aikatan tsaro na makarantu 1,600 zuwa makarantun sakandare a fadin jihar, a wani bangare na kokarin karfafa tsaron makarantun jihar.

Matakin ya biyo bayan sace dalibai mata 25 da aka yi a Jihar Kebbi kwanan nan.

Gwamnan, a ranar Talata, ya kaddamar da rabon takardun daukar aiki na dindindin ga sabbin ma’aikatan.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya tarbi tagwayen da aka haifa a haɗe, bayan an yi aikin raba su a Saudiyya

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, Gwamna Yusuf ya bayyana wannan mataki na tura jami’an tsaron makarantu da yawa a lokaci guda a matsayin “muhimmin mataki wajen dawo da tsaro da daidaito a makarantu.”

Ya jaddada cewa ba za a iya samun ingantaccen karatu ba idan tsaro yana cikin hadari.

Gwamnan ya ce masu sa-idon za su kasance layin kariya na farko ga dalibai, malamai da kayayyakin makaranta ta hanyar sa ido kan zirga-zirgar da ba ta dace ba, dakile barazanar da ka iya tasowa da kuma tallafa wa ingantaccen gudanar da harkokin karatu.

Leave a Reply