Gwamnan Kano ya sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar

0
57
Gwamnan Kano ya sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar

Gwamnan Kano ya sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar

Daga Ali Sanni

Gwamna Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sassauta dokar nana fita a kano zuwa awa 12.

Idan zaku tuna gwamnatin jihar ta Kano ta sanya dokar kullen ne sakamakon wasu ɓata-gari da sukayi anfani da zanga-zangar dake gudanar a jihar wajen kawo tashin hankali da satar duniyoyin mutane.

Kwamishina ‘yan sandar jihar ta Kano, Gogo Salman, ne ya sanar da sassauta dokar a ranar talata bayan tattaunawa da hukumar ta tsaro tayi da gwamnatin jihar.

Salman ya ƙara da cewa ‘yan sandar jihar zasu cigaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar tare da kamawa da hukunta duk wanda yayi yunkurin kawo tashin hankali a jihar.

KU KUMA KARANTA: Wata kotu a Kano ta tura masu zanga-zanga 632 gidan gyaran hali

Ya ƙara da cewa sassauta dokar hana fitan ta biyu bayan ganin an samu kwanciyar hankali a jihar a taron masu ruwa da tsaki na harkar tsaro da sukayi da gwamnatin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci mazauna jihar tasa da su guji aikata abunda zai kawo tashin hankali ko tarzoma a jihar sannan so ba ma’aikatan tsaro haɗin kai wajan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.