Gwamnan Kano ya naɗa sababbin sarakuna 3

0
82
Gwamnan Kano ya naɗa sababbin sarakuna 3

Gwamnan Kano ya naɗa sababbin sarakuna 3

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa sababbin sarakuna masu daraja ta biyu a jihar.

Waɗanda aka naɗa ɗin su ne Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda kafin naɗinsa shi ne tsohon Sarkin Masarautar Gaya da aka rushe.

Sai Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Rogo.

Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Bunkure.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan na Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce naɗin ya fara aiki nan take.

“Yayin da yake musu murna bisa naɗin, Gwmana Abba ya yi ƙira a gare su su kasance masu kiyaye al’adu da zaman lafiya da haɗin kan jama’arsu.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta haramta wa Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

A ranar Talata ne Gwamna Abba ya sanya hannu kan sabuwar dokar Masarautun Kano wacce ta ƙirƙiri Masarautun Gaya da Rano da Ƙaraye masu daraja ta biyu.

Gwamnan ya saya hannu kan sabuwa dokar ne ‘yan sa’o’i bayan Majalisar Dokokin Jihar ta amince da sabuwar Dokar Masarautun a ranar Talata.

Sababbin masarautun za su ƙunshi wasu ƙananan hukumomi ne a ƙarƙashinsu, sai dai ya yawan ƙasashen hakiman bai kai na tsofaffin masarautun da aka rushe ba.

Sanarwar da Sanusi Bature ya fitar ta ce a yanzu “Masarautar Gaya za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu ne kawai. Rano za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure kawai, yayin da Ƙaraye za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Ƙaraye da Rogo kawai.”

Naɗa sabbin sarakunan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tirka-tirka kan dokar da gwamnatin jihar ta sanya wa hannu ta rushe masarautu hudu na Gaya da Rano da Karaye da kuma Bichi, da sauke Sarki Aminu Ado Bayero da kuma mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na II.

Leave a Reply