Gwamnan Kano ya naɗa sabon sakataren gwamnatin jihar
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar, SSG.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a daren jiya Asabar ta ce nadin na Ibrahim zai fara aiki daga ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu, 2025.
KU KUMA KARANTA:Za mu yi bincike kan kisan da aka yi wa mutane a Rimin Zakara – Gwamnatin Kano
Sanarwar ta ce, an zabi Ibrahim ne bisa la’akari da gogewar da ya ke da ita, wadanda ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati da kuma tabbatar da jihar kan turba da manufofinta na ci gaba.
Ya ce Ibrahim zai yi amfani da gigewar sa a aikin gwamnati ta tsawon shekaru talatin a sabon aikin nasa.
Tun daga 1987 zuwa 2023, ya samu muhimman mukamai na shugabanci wadanda su ka ba da gudunmawa sosai ga tsarin mulki da gudanar da mulki a jihar Kano.
Daga watan Maris ɗin 2001 zuwa Mayu 2015, Ibrahim ya yi aiki a matsayin babban sakatare na fannin bincike, tantancewa, da harkokin siyasa a ofishin sakataren gwamnatin jiha.