Gwamnan Kano, ya karɓi baƙuncin takwaransa na Katsina Dikko Raɗɗa
Daga Idris Umar,Zariya
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya karɓi baƙuncin takwaransa na Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD CON FNAH a Fadar Gwamnatin Jihar Kano.
KU KUMA KARANTA:Rundunar ‘yansanda ta ƙasa ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano Sanusi II
Inda Gwamnan na Jihar Katsina ya kawo ziyara Jihar Kano domin miƙa saƙon Ta’aziyyarsa da Gwamnatinsa da Al’umar Jihar Katsina ga Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa ga rashin Marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi wanda ALLAH yaiwa rasuwa.









