Gwamnan Kano ya bawa masarautu umarnin fara shirye-shiryen hawan bukin ƙaramar Sallah

0
147
Gwamnan Kano ya bawa masarautu umarnin fara shirye-shiryen hawan bukin ƙaramar Sallah

Gwamnan Kano ya bawa masarautu umarnin fara shirye-shiryen hawan bukin ƙaramar Sallah

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnan Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkan masarautu hudu a jihar da su fara shirye-shiryen hawan sallah.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a wata sanarwa da ya fitar ya ce gwamnan ya bada umarnin ne yayin da ya yi buɗe-baki da Sarakuna hudu na jihar, karkashin jagorancin Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi ll a daren jiya Talata a fadar gwamnatin Kano.

A cewar gwamnan, al’ummar Kano sun ƙagu lokacin Sallah ya zo su ci kwalliya su je kwallon hawa don samun nishadi daga al’adun jihar.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya karrama zakarun gasar karatun Alƙur’ani, ya ba su kujerun aikin Hajji

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ba za ta bari wani abu ya gindaya da zai hana mazauna jihar samun wannan dama ta bikin sallah ba.

Ya bayyana cewa akwai shiri da aka tanada ta yadda jami’an tsaro za su bada kariya da tabbatar da cewa an yi bukukuwan sallah lami lafiya a jihar ba tare da wasu ɓatagari sun kawo cikas ba.

Leave a Reply