Gwamnan Kano ya ƙaddamar da ayyukan gadar gadojin sama a jihar

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da aikin Gadar Kofar Ɗan Agundi duk da cewa kotu ta hana shi amfani da kuɗin ƙananan hukumomi.

Alfijir labarai ta rawaito ranar Juma a nan ne Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da aikin Gadar Tal’udu a kan biliyan 14.45 da kuma Gadar Ɗan Agundi wanda za a aiwatar a kan kuɗi naira biliyan 15.9 a bisa tsarin haɗaka tsakanin ƙananan hukumomi da matakan gwamnatin jihar.

Gwamna Abba ya bayyana cewa ayyukan biyu za su kawo bunƙasar arziki a jihar da kuma rage cunkoson ababen hawa a yankunan da aka sanya gadoji.

KU KUMA KARANTA: Shugabannin ƙananan hukumomi sun maka Gwamnatin Kano a gaban ƙuliya

Gwamnan ya ƙaddamar da aikin ne bayan wata Kotun Tarayya ta hana gwamnatin jihar amfani da kuɗin ƙananan hukumomi a aikin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *