Gwamna Yobe ya amince da ƙarin wa’adin watanni 2 da a miƙa rahoton tantance ma’aikatan jihar
Daga Ibraheem El-Tafseer
Kwamitin tantance sunayen ma’aikata na jihar Yobe ya miƙa rahotonsa ga shugaban ma’aikata, Alhaji Tonga Betara Bularafa, inda ya bayyana gagarumin giɓi wajen tantance ma’aikatan.
Kwamitin wanda babban sakataren dindindin na ofishin kula da ma’aikata, Dakta Bukar Kilo ya jagoranta, an umurce shi da ya tabbatar da bayanan ma’aikatan tare da tabbatar da sahihancinsa. A lokacin atisayen na watanni tara, ma’aikatan gwamnati 27,111 ne kawai daga cikin 32,140 suka bi aikin tantancewar, inda har yanzu ma’aikata 5,029 ba su mika fom ɗinsu na ‘Bio-Data’ ba.
Dakta Kilo ya ba da shawarar kafa kwamitin tantancewa don magance saɓanin. Ya ce dole ne ma’aikatan da ba su bi ƙa’ida ba su gabatar da takardun shaidarsu na asali, da bayanan ɗaukar aiki, da kuma bayanan banki na watanni shida don tabbatar da aikinsu. Rashin yin biyayya zai haifar da dakatar da albashi.
“Wannan matakin yana da mahimmanci don tabbatar da daidaito da gaskiya a cikin bayanan ma’aikata na gwamnati,” in ji Dakta Kilo.
KU KUMA KARANTA:Watan Ramadan: Gwamnan Yobe ya ƙaddamar da raba buhunan shinkafa dubu 35
Da yake karɓar rahoton, Alhaji Tonga Betara Bularafa ya yabawa kwamitin bisa ƙoƙarinsa amma ya lura da matsalolin da ba a warware ba da ke buƙatar ci gaba da bincike.
Domin magance waɗannan ƙalubalen, Gwamna Mai Mala Buni ya amince da tsawaita wa’adin watanni biyu ga ma’aikatan gwamnati su miƙa bayanansu na ɗaukar aiki ‘Bio-Data’.
“Ya kamata ma’aikatan gwamnati su yi amfani da wannan damar, domin rashin yin hakan zai jawo mummunan sakamako,” in ji Shugaban Ma’aikata.
Ana sa ran tsawaita wa’adin zai baiwa gwamnatin jihar damar kammala tantance sunayen da aka zaɓa tare da tabbatar da ingantaccen aikin ma’aikata.