Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya amince da sauya sunayen wasu manyan makarantun jihar guda takwas, da sunayen gwarazan jihar.
A cewar kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Aƙibu Ɗalhatu, matakin ya samo asali ne daga yadda gwamnatin ke matuƙar girmama abubuwan tunawa da nasarorin da manyan jaruman jihar Sokoto suka yi.
Majalisar zartarwar jihar ta kammala wannan matsayar ne a zamanta na ranar 17 ga watan Mayu, inda ta sanar da cewa “gwamnatin jihar ta yi imanin cewa waɗannan mutane sun cancanci a girmama su da kuma tunawa da su har abada saboda irin gudunmawar da suka bayar a ɓangarori daban-daban na jihar da ma ƙasa baki ɗaya.”
KU KUMA KARANTA: Babu Wani Bangare Da Ya Samu Matsala A Jihar Sakkwato – Tambuwal
Cibiyoyin gwamnati da aka canza wa suna: Jami’ar Jihar Sakkwato, wadda aka canza wa suna Jami’ar Sheikh Abdullahi Fodio, don karrama Sheikh Abdullahi Fodio; Jami’ar Ilimi ta Jihar Sakkwato, wadda aka canza wa suna Jami’ar Ilimi ta Shehu Shagari don karrama Shehu Shagari; Kwalejin Ilimi, wacce aka canza wa suna Kwalejin Ilimi ta Sultan Ibrahim Dasuƙi don karrama Sultan Ibrahim Dasuƙi; da kuma sabon asibitin koyarwa da aka gina mai suna Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar Teaching Hospital don karrama Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.
Sauran sun haɗa da Kwalejin Noma da Kimiyyar Dabbobi, wadda aka canzawa suna zuwa Ambasada Shehu Malami Kwalejin Noma da Dabbobi don karrama Ambasada Shehu Malami; Kwalejin Kimiyyar Ma’aikatan Jinya, wadda aka canza wa suna Balaraba Buda College of Nursing Sciences don girmama Balaraba Buda; Kwalejin Ungozoma wadda aka canza wa suna Aisha Ahmad Gandi College of Midwifery don karrama Aisha Ahmad Gandi; Kwalejin Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci, wacce aka canza wa suna Haliru Binji College of Legal and Islamic Studies, don karrama Haliru Binji.
Ɗalhatu ya ƙara da cewa Tambuwal ya shahara ne a bisa jajircewarsa na bunƙasa ilimi kuma “wannan shawara ce ta haɗin gwiwa don kiyaye al’adun gargajiya da kuma zaburar da al’ummar da za su zo nan gaba su yi koyi da jiga-jigan da suka bar wa al’umma tarihi.”
“An gudanar da ingantaccen tsarin sake suna tare da matuƙar tunani da fahimta.
Ta hanyar tattaunawa da manyan masana tarihi, manyan shugabannin al’umma, da wakilai daga sassa daban-daban, gwamnati ta tabbatar da cewa zaɓaɓɓun sunayen sun fito da kyawawan ɗabi’u da kyawawan manufofin da jihar Sakkwato take da shi,” ya ƙara da cewa.
Tambuwal ya mika ƙira ga ɗaukacin al’ummar jihar Sakkwato da su rungumi wannan gagarumin ƙuduri tare da buɗaɗɗiyar zuciya da kuma karɓuwa.
Ya bayyana cewa gwamnati na da yaƙinin cewa sauya sunayen makarantun ilimi ya zama babban nuna godiya ga sadaukarwar da waɗannan jarumai suka yi domin ci gaban jihar Sakkwato da ci gaban jihar.