Gwamna Buni ya ƙaddamar da aikin titin Gashuwa zuwa Masaba da Karasuwa zuwa Galu

0
512

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da aikin gina titin Gashua-Masaba mai tsawon kilomita 29.5 a jihar Yobe.

Buni ya ce, gina waɗannan hanyoyi a jihar ci gaba ne da ƙoƙarin gwamnati na samar da ababen more rayuwa don buɗe al’ummar jihar domin ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙi da wadata.

Ya lura cewa, hanyar idan aka kammala za ta inganta sauƙin jigilar kayayyaki da ayyuka zuwa ga al’ummomin da ke da fa’ida musamman, amfanin gona kamar gero, masarar, wake, Riɗi da ‘ya’yan kankana, da dai sauransu, waɗanda ake samarwa da yawa na kasuwanci.

Gwamnan ya bayyana cewa, aikin titin kwalta na Gashua zuwa Masaba mai tsawon kilomita 25 da aikin titin Karasuwa zuwa Galu mai tsawon kilomita 4.5 ya yi daidai da ƙudurin gwamnatin jihar da yunƙurin samar da hanyoyin sadarwa masu kyau a faɗin jihar Yobe.

KU KUMA KARANTA: Za mu gyara hanyoyin tuƙa kekuna a babban birnin tarayya Abuja – FCTA

“Gwamnatin jihar Yobe ta himmatu matuƙa wajen gudanar da wannan aiki domin bayar da tallafi ga matsalar sufuri da jama’a ke fama da su a yankin.

“A bisa la’akari da muhimmancin aikin ne gwamnatin jihar ta ƙaddamar da aikin neman ’yan kwangilar da suka yi suna wanda ya kawo ƙarshen zaɓar kamfanin ‘Maduwa Road Construction Ltd’ na Gashua zuwa Masaba da ‘Greyland Multipurpose Investment Limited’ domin gudanar da ayyukan titin Karasuwa zuwa Galu,” inji Gwamna Buni.

Buni ya ci gaba da cewa, aikin titin Gashua zuwa Masaba ana bayar da shi ne a kan kuɗi naira biliyan 4.4, yayin da na karasuwa zuwa Galu kuma an bayar da shi a kan kuɗi Naira biliyan 1.3 tare da kammala ayyukan a watanni 9.

Ya kuma yi ƙira ga kamfanonin da su bi ƙa’idojin kwangila da gwamnatin jihar Yobe ta bayar, sannan kuma ya umurci ma’aikatar ayyuka ta jihar da ta gudanar da sahihin kulawa domin gwamnati ta samu ƙimar kuɗinta.

Leave a Reply