Gwamna Abba ya raba wa ƙananan manoma kyautar takin zamani
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon takin zamani na sama da Naira biliyan daya ga kananan manoma da suka haɗa da mata da masu buƙata ta musamman a jihar.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya raba wa manema labarai, ya ce shirin wani mataki ne na cika alƙawarin da gwamnan ya dauka a yaƙin neman zaɓe na inganta rayuwa ta hanyar saka hannun jari a harkar noma.
A cewar Sanusi Bature, Gwamnan ya raba takin ne kyauta ga manoman don rage musu raɗaɗin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.
Idan za a iya tunawa Gwamna Yusuf a lokacin yakin neman zaɓensa a 2023 ya yi alƙawarin kawo sauyi a harkar noma ta hanyar samar da ingantattun kayan aikin noma masu arha kamar yadda yake ƙunshe a cikin kundin manufofinsa da ke shafi na 70 da ya gabatar wa Kanawa mai taken “Alƙawarina ga Kanawa.”
KU KUMA KARANTA: Gwamna Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II Sarautar Kano
Dawakin-Tofa ya bayyana cewa takin zamani samfurin NPK na sama da Naira biliyan daya an raba wa ƙananan manoma 52,800 a faɗin ƙananan hukumomi 44 , wanda kamfanin samar da kayan noma na jihar Kano (KASCO) ya samar.
Da yake ƙaddamar da rabon takin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne da nufin rage tsadar kayan noma da kuma bunƙasa samar da abinci a Jihar kano.
Ya ce Majalisar Zartaswar jihar ta kuma amince da sayo takin zamani na sama da Naira biliyan biyar wanda nan ba da dadewa ba za a samar wa manoman Kano a farashi mai sauƙi.
Ya jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da samar da abinci ta hanyar samar da taki a kai a kai wanda kamfanin KASCO mallakar jihar zai rika yi.
Ya ce gwamnati na inganta kamfanin KASCO da sauran cibiyoyin masana’antu na jihar don dawo da hanyoyin samun kudaden shiga da kuma ɗorewar tattalin arzikin jihar.
Waɗanda suka samu tallafin da suka hada da mata manoma da masu bukata ta musamman ana sa ran za su samu kilo 25 na takin NPK don tallafa wa ayyukan noma da kuma bunkasa noma don inganta rayuwar al’umma.