Gobe Asabar za a fara Azumin watan Ramadan a Najeriya – Fadar Sarkin Musulmi
Daga Ibraheem El-Tafseer
Fadar mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da maraicen ranar Juma’a.
Cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmin, Alhaji Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban.
KU KUMA KARANTA:Gwamnan Yobe ya yi ƙira ga jami’an tsaro da su tsaurara tsaro a watan Ramadan
Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446 (2025).
Tuni dai hukumomin Saudiyya suka sanar da ganin watan a ƙasar, inda suka ayyana gobe Asabar a matsayin ɗaya ga watan Ramadan a Saudiyya.