Gobara ta tashi a hedikwatar ‘yan sanda a ƙasar Masar, ta raunata mutane da dama

Wata babbar gobara ta tashi a hedikwatar ‘yan sanda a birnin Ismailia na ƙasar Masar a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, inda ta raunata aƙalla mutane 38 kafin a kashe ta, a cewar ma’aikatar lafiya.

Kakakin ‘yan sandan ya ce an yi wa wasu daga cikin waɗanda suka jikkata magani a wurin, yayin da wasu kuma aka kai su asibiti.

Ba a dai bayyana musabbabin tashin gobarar a ginin da ke Ismailia ba, in ji jami’ai.

Aƙalla motocin ɗaukar marasa lafiya 50 da jirage biyu ne aka aika zuwa wurin.

Daga cikin mutane 26 da suka samu raunuka waɗanda aka kai su wani asibiti na yankin, 24 sun yi fama da “asphyxia” an yi wa wasu mutum biyu magani sakamakon ƙonewa, in ji ma’aikatar lafiya. An yi wa wasu 12 magani a wurin.

Ministan cikin gida Mahmoud Tawfik ya ba da umarnin gudanar da bincike kan musabbabin gobarar a ginin, in ji wata sanarwa da ma’aikatarsa ​​ta fitar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *