Gobara ta ƙone shaguna da dama a kusa da babban masallacin Zariya

0
186

Wata gobara ta ƙone kaya na dubban Nairori a wasu shaguna da ke gefen masallacin Ƙofar Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Masu shagunan sun yi zargin wutar da ta fara ci tun misalin ƙarfe 2:00 na daren Juma’a, ta ɗauki kusan sa’o’i 5 tana ci ba tare da kai ɗaukin gaggawa daga jami’an kashe gobara ba.

Da yake ƙarin haske kan faruwar lamarin, Kabir Ibrahim Wazirin Kasuwa ya yi zargin cewa wutar lantarkin da aka kawo misalin ƙarfe 2:09 na dare ce ake kyautata zaton ta sabbaba farawar lamarin.

Ya kuma ce duk ƙoƙarin da suka yi na kai rahoto ga jami’an kwana-kwana domin su kai musu ɗauki, ya ci tura saboda wasu matsalolin da suke fuskanta.

KU KUMA KARANTA: Amarya da mai juna biyu sun mutu a gobarar matatar mai a Ribas

Sai dai ya yaba wa ƙoƙarin da jami’an tsaro da sauran al’umma suka yi na ba su kulawar da ya kamata lokacin faruwar lamarin.

Kabir Wazirin Kasuwa ya ce sun yi asarar kaya na maƙudan kuɗaɗe wanda kuma suke buƙatar agajin gaggawa daga hukumomin da lamarin ya rataya kan su

Ya kuma buƙaci samar da ƙarin kulawa ga hukumomin da ke kula da kashe gobara don kai ɗaukin gaggawa lokacin da bukatar hakan ya taso.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin Kwamandan Kashe Gobara Mai kula da shiya ta ɗaya Ummar Mohammad ya ci tura, kasancewar ba ya ofishinsa kuma lambar wayarsa ba ta shiga.

Amma wani jami’i a hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce suna fuskantar matsaloli na rashin isasshen man motar, inda ya ce wani lokacin ma har da rashin shi kansa ruwan da za su yi amfani da shi wajen kashe gobara idan aka kai musu rahoto irin haka.

Ya ƙara da cewa suna fuskantar waɗannan matsalolin ne a daidai lokacin da aka fara shiga yanayin hunturu, wanda aka fi barazanar samun tashin gobara.

Leave a Reply