Gobara ta ƙone kayayyakin naira biliyan uku a Aba

3
387

Wata gobara da ta tashi a daren ranar asabar da ta gabata ta ƙone kayayyakin fata da kayan aiki da injina da aka ƙiyasta sama da naira biliyan uku a garin Aba dake jihar Abiya.

Gobarar ta shafi shaguna sama da 30 a unguwar Mansion Zone na rukunin masana’antu na Fata na Powerline.

Shugaban rukunin da abin ya shafa a rukunin masana’antu, Ugochukwu Nwachukwu ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Lahadi cewa sama da ma’aikata 500 ne ke aiki a shagunan da abin ya shafa.

KU KUMA KARANTA: Hukumar kashe gobara ta Kano ta ceci rayuka 26 da kuɗi naira miliyan 17

Mista Nwanchukwu ya ce ko da yake hukumar kashe gobara ta Abia ta zo daga Umuahia kimanin sa’a guda bayan tashin gobarar, amma ƙoƙarin da suka yi ya taimaka wajen kashe gobarar.

Cherechi Ndukwe, wanda abin ya shafa, ya ce ya garzaya wurin ne bayan da ya yi waya game da lamarin.

“Mun yi iya bakin ƙoƙarinmu amma ba mu yi nasara ba don murƙushe gobarar da buhunan ruwa kafin zuwan mutanen ‘Abia Fire Service’ daga Umuahia.

Ya ƙara da cewa “Jami’an kashe gobara sun isa ‘yan mintuna da ƙarfe 11 na dare don taimaka mana mu kashe gobarar,” in ji shi.

Ndukwe ta roƙi taimakon gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, saboda lamarin ya jefa kasuwancinsu da iyalansu da ma’aikatansu cikin haɗari.

Ya ƙara da cewa “Zai yi matuƙar wahala a rayu ba tare da goyon bayan Abia da gwamnatin tarayya ba.”

Wata da abin ya shafa, Nnenna Onyedikachi, ta ce duk abin da suka saka a cikin kasuwancin gobarar ta lalata su.

Tsohon shugaban ƙungiyar masu sana’ar takalmi ta Omenka, shiyyar Powerline, Goodluck Mmeri ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda ’yan ɓata-gari suka yi amfani da lamarin wajen sace wasu kayan da injina.

Har ila yau, Mazi Okechukwu Williams, shugaban ƙungiyar masu sana’ar fata a jihar Abia, ya koka kan irin ɗimbim asarar da ‘yan kasuwar suka yi a halin da ake ciki a halin yanzu na tattalin arziƙi.

Ya yi nadama kan yadda har yanzu gwamnatin jihar ba ta sake kafa cibiyar kula da kashe gobara a kasuwar Aria International Market domin shawo kan matsalar gobara.

Williams ya roƙi Gwamna Alex Otti da ya maido da ofishin hukumar kashe gobara don tabbatar da ɗaukar matakin gaggawa kan duk wata gobara da ta tashi a kasuwa da kewaye.

3 COMMENTS

Leave a Reply