Gasar AFCON 2025: Najeriya ta fasa fafatawa da Libya
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta ce ba za ta fafata da Libya ba a wasan ranar Talata na neman cancantar shiga gasar AFCON 2025 saboda hukumomin ƙasar sun sauya filin da ya kamata jirgin tawagar ya sauƙa da kuma hana tawagar shiga cikin ƙasar inda ‘yan wasa da sauran jami’ai suka kwashe fiye da sa’o’i 12 suna zaman jira.
”Tawagar Najeriya da za ta buga wasa da Libya na neman cancantar shiga gasar AFCON 2025 ranar Talata ta kwashe awanni 12 a filin jirgin saman Al Abraq bayan ta sauka a Libya,” in ji wata sanarwa da hukumar kula da ƙwallon ƙafar Najeriya (NFF) ta fitar ranar Litinin da safe.
Tawagar ta Najeriya ta isa Libya ranar Lahadi gabanin fafatawar, amma ta yi ƙorafi cewa an bar su ba tare da sanin halin da ake ciki ba duk da cewa an canza inda jirginsu zai sauka daga filin jirgin saman Benghazi zuwa filin jirgin saman Al Abraq.
”A wani mataki mai ɗaure kai, an bar jirgin da muka yi haya ValueJet yana waɗari cikin yanayi mai hatsari, kana an sauya masa wurin sauka zuwa ƙaramin filin jirgi daga filin jirgin saman Benghazi a lokacin da direba ya kammala shirin sauka a Benghazi,” in ji NFF.
KU KUMA KARANTA: Najeriya ta naɗa Finidi George sabon kocin Super Eagles
Hakan ne ya sa ‘yan wasa “suka yanke shawarar ƙin buga wasan kuma jami’an NFF sun soma shirye-shirye domin mayar da su gida,” a cewar sanarwar.
Shi ma kyaftin ɗin Super Eagles, William Troost-Ekong ya wallafa saƙo a shafinsa na X inda ya bayyana ce shi da sauran ‘yan wasan Najeriya sun yanke shawarar ƙin buga wasa da Libya.
Troost-Ekong ya nuna rashin jin daɗinsa game da mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki bayan isar su Libya.
Kawo yanzu, hukumomi a Libya ba su ce komai ba game da wannan lamari.
Tawagar Najeriya ta je Libya ne domin fafatawa da Libya a zagaye na biyu na wasan, kwanaki kaɗan bayan ta doke tawagar Libya da ci 1-0 a wasan da suka yi a filin wasa na Uyo a jihar Akwa Ibom.