Gasar AFCON 2025: CAF za ta binciki halin da ‘yan Super Eagles suka fuskanta a filin jirgin Libya

0
38
Gasar AFCON 2025: CAF za ta binciki halin da 'yan Super Eagles suka fuskanta a filin jirgin Libya

Gasar AFCON 2025: CAF za ta binciki halin da ‘yan Super Eagles suka fuskanta a filin jirgin Libya

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta ƙaddamar da bincike kan abin da ya sa tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta ƙi buga wasan neman shiga gasar AFCON da Libya inda suka ambaci “wulaƙancin” da aka yi musu a filin jirgin sama na Libya.

A wata sanarwa da CAF ta fitar ranar Litinin, ta ce “tana tattaunawa da hukumomin Najeriya da na Libya bayan an sanar da ita cewa an yi watsi da tawagar ta ‘yan wasan Najeriya (Super Eagles) da masu horar da su, an kuma bar su cikin mawuyacin hali tsawon sa’o’i a wani filin jirgin sama, wanda hukumomin Libya suka umarce su su sauka.”

CAF ta ƙara da cewa: “An miƙa batun ga Hukumar Ladabtarwa ta CAF domin bincike, kuma za a ɗauki matakan da suka dace kan duk waɗanda suka saɓa Matakan CAF da Dokokinta.”

‘Yan wasan na Najeriya sun ce an yi watsi da su a filin jirgin sama na Libya tsawon fiye da awa 12 a ranar Litinin. Sun sauka a nisan kilomita 200 daga masaukinsu.

KU KUMA KARANTA: Gasar AFCON 2025: Najeriya ta fasa fafatawa da Libya

‘Yan wasan na Super Eagles da ma’aikata sun tashi zuwa Libya ranar Lahadi da daddare, sai dai an karkatar da jirginsu zuwa filin jirgin sama na Al Abraq na Ƙasa-da-Ƙasa, maimakon na Benghazi inda da farko nan aka tsara za su sauka, wanda ya zarce nisan kilomita 200, kuma sai an yi tafiyar awa uku da rabi kafin a je otal ɗinsu.

Ɗaya daga jami’an Filin Jirgin Saman na Al Abraq na Ƙasa-da-Ƙasa ya shaida wa manema labarai cewa tawagar ta Najeriya ta ƙi buga wasan ne a Libya don ƙaurace wa wasan neman shiga gasar AFCON da Libya a ranar Talata.

Jami’in ya ce ‘yan wasan na Najeriya sun yanke hukuncin koma wa gida ne maimakon buga wasan. Wasu daga ‘yan wasan sun yi zargin cewa an bar su ba tare da abinci da ruwa ba.

Ita ma tawagar ‘yan wasan Libya ta fuskanci irin wannan yanayi gabanin wasan neman shiga Gasar ta AFCON a Nigeria ranar 11 ga watan Oktoba, kamar yadda rahotannin kafofin watsa labaran Libya suka nuna.

Rahotannin sun ce “an sauƙe tawagar Najeriya a filin jirgin Al Abraq “a matsayin ramuwar gayya.”
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Libya (LFF) ta mayar da martani kan jinkirin da tawagar Najeriya ta fuskanta, inda ta ce matsaloli ne da aka saba fuskanta na sauƙa da tashi da na aiki suka janyo shi.

“Muna musanta duk wani zargi na cewa da gangan aka tsara lamarin ko kuma akwai wata manufa kan abin da ya faru,” a cewar LFF.

Leave a Reply