Connect with us

Ƙasashen Waje

Fiye da kashi 95 na al’ummar Sudan ba sa iya samun abinci sau ɗaya a rana – WFP

Published

on

Watanni 10 kenan da yaƙin da ya jefa ƙasar Sudan ga “kusan rugujewa”, akasarin mutanen ƙasar na cikin yunwa, kamar yadda Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

“A wannan lokacin, ƙasa da kashi biyar cikin 100 na ‘yan Sudan ke iya samun cin abinci sau ɗaya a rana,” kamar yaddai daraktan hukumar WFP na Sudan, Eddie Rowe, ya shaida wa manema labarai ranar Laraba a Brussels.

Tun a watan Afrilun da ya gabata ne Sudan ke fama da yaƙi tsakanin rundunar sojin ƙasar da dakarun sa kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da haifar da abin da MƊD ta kira “rikicin gudun hijira mafi girma a duniya”.

Kimanin mutum miliyan 10.7 ne yaƙin da ake fama da shi a yanzu da kuma rikice-rikicen da ya ɓarke a baya ya raba da muhallansu, a cewar MƊD.

KU KUMA KARANTA: Matsalar ƙarancin abinci za ta ta’azzara a Sudan saboda fari — MƊD

Mutum miliyan tara ne suka rasa matsugunansu a cikin Sudan, inda Rowe ya ce “mummunar ta’azzarar rikicin da tashe-tashen hankula, da dakatar da girbin amfanin gona da yawaitar gudun hijira na ci gaba da jefa miliyoyin mutane cikin wani bala’i na jinƙai.”

A duk faɗin ƙasar Sudan, wanda hukumar ta WFP ta ce tuni ta fuskanci matsalar karancin abinci a duniya kafin yakin, mutane miliyan 18 na fuskantar matsalar rashin abinci a yanzu haka.

Daga cikin waɗannan, Rowe ya ce “kusan miliyan biyar na gab da fuskantar bala’i” — suna fama da ɗaya daga cikin mafi munin matakin gaggawa da WFP ke amfani da shi, na biyu bayan yunwa.

Ƙungiyoyin ba da agaji sun kwashe watanni suna gargaɗin cewa, sakamakon cikas ga ayyukan jinƙai da kuma ƙarancin kudade, lamarin yunwa ya afka wa Sudan.

Amma irin wannan cikas na isar da agaji suna hana iya tantance girman bala’in.

A cewar Michael Dunford, daraktan yankin gabashin Afirka na WFP, akwai babban batu a cikin “samuwar bayanan don tabbatar da cewa an cimma matsayar da ake bukata don ayyana fari ko a’a”.

Yayin da WFP ke iya kai kashi 10 cikin 100 na kayan agaji ga masu buƙata, “akwai manyan sassan ƙasar da ba za mu iya shiga ba,” Dunford ya shaida wa manema labarai.

Yankunan da suka fi albarka a Sudan sun taimaka wajen kawar da yunwa, idan ba don faɗan ya mamaye yankunan noma na kasar ba.

A cikin watan Disamban 2023, wani kutse da dakarun soji suka sake yi ya sa yaƙin ya kai har zuwa jihar Al Jazira da ke kudu da Khartoum babban birnin kasar, inda aka shirya samar da mafi yawan hatsin Sudan a kakar bana.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Published

on

Harin ta'addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Wani hari da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne suka kai ƙauyen Djiguibombo da ke kusa da garin Bandiagara a yankin tsakiyar ƙasar Mali, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 20, kamar yadda wasu hukumomin yankin biyu suka tabbatar.

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun tabbatar da mutuwar mutane 20, sannan suka ce yadda lamuran tsaro suka taɓarɓare a yankin, ya hana jami’an tsaro kai ɗauki wajen.

Wani jagoran matasan yankin shi ma da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun a farkon daren ranar Litinin ɗin data gabata ne maharan suka kai farmakin, inda suka kwashe tsawon sa’oi uku a cikin garin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai

Ya ce sama da mutane 20 ne aka kashe a harin, kuma fiye da rabinsu matasa ne inda aka ranke musu harsuna.

Kasar Mali dai na fama da matsalolin tsaro na ƙungiyar Al-Qaeda da kuma na IS tun a shekarar 2012, inda ya bazu kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da ita.

Tun bayan ƙwace mulki da sojoji suka yi a kasar a shekarar 2020, hukumomi  ke jin tsoron fitowa fili su sanar da labarin hare-haren ta’addancin da ake kai wa kasar da ke Yammacin Afrika.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Published

on

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama - Ministan Tsaron Isra'ila

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra’ila za su kasance a shirye don daukar duk wani matakin da ya dace kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon, ko da yake abin da ake so shi ne cimma matsaya ta shawarwari.

Muna kai wa ƙungiyar Hizbullah hari sosai a kowace rana kuma za mu kai ga cikakken shiri na ɗaukar duk wani mataki da ake buƙata a ƙasar Labanon, ko kuma cimma wani shiri daga matsayi mai ƙarfi.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

Mun fi son tsari, amma idan aka kai mu maƙura za mu san yadda za mu yi yaƙi,” an ruwaito Gallant a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Published

on

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Aƙalla mutum 12 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a jiya Laraba a wani hari da aka kai kan wata kasuwar dabbobi da ke El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Yammacin Sudan.

A wata sanarwa da kwamitin sulhu na kwamitocin ‘yan gwagwarmaya na El Fasher ya fitar ya ce “harbin bindigogi a kasuwar dabbobi da ke birnin El Fasher ya yi sanadin mutuwar fararen hula 12 da kuma wasu 20 da suka samu raunuka daban-daban.”

Tun da fari a ranar Larabar da safe, kwamitocin ‘yan gwagwarmaya sun ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai mummunan hari El Fasher da manyan bindigogi.

Tun a ranar 10 ga Mayu, aka fara ƙazamin fada tsakanin sojojin Sudan da RSF a El Fasher. Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ke amfani da birnin a matsayin cibiyar ayyukan jinƙai ga yankin Darfur.

Rikicin Sudan ya ɓarke ne a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan yarjejeniyar shigar da RSF cikin rundunar soja.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

Ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 16,000, da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, sannan sama da miliyan 25 na buƙatar agajin jinƙai, lamarin da ya zama mafi girma a duniya ta ɓangaren matsalar rashin matsuguni da yunwa, a cewar MƊD.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like